Home Labarai Kano: Sabuwar gobarar da ta tashi a Kasuwar Dakata ta ƙone Shaguna...

Kano: Sabuwar gobarar da ta tashi a Kasuwar Dakata ta ƙone Shaguna 50

0

Rahotonni sun bayyana cewa, akalla shaguna 50 ne suka ƙone sakamakon gobara da ta tashi da Asuba a kasuwar Kwalemar Fatima Simra da ke unguwar Dakata, yankin Karamar Hukumar Nassarawa a jihar Kano a yau Juma’a.

Shaidun gani da ido sun bayyana wa manema labarai cewa, gobarar, wadda aka ce ta fara ne kimanin ƙarfe 5:40 na safe, ta bar ’yan kasuwa na kididdige asarar su yayin da kaya da dukiya da darajarsu ta kai miliyoyin naira suka salwanta cikin wuta.

Shugaban kwamitin gobarar kasuwar, Dauda Haruna Chula, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ya yi da manema labarai.

Ya bayyana cewa yawancin shagunan da abin ya shafa na kanana ne, wadanda ke harkar sarrafa mai da kuma sake yin amfani da robobi da leda.

A cewarsa, gobarar tana ci gaba da ruruwa a lokacin da yake magana.

“Daga abin da muka gani a farko, kusan shaguna 50 sun riga sun kone, kuma gobarar tana ci gaba. Har yanzu muna jiran jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano,” in ji Chula kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Chula ya kara da cewa jami’an kasuwar sun gaggauta sanar da hukumomin agaji da suka dace da zarar sun lura da tashin gobarar.

“Mun yi iya kokarinmu wajen kiran su da sanar da su halin da ake ciki. Yanzu haka ma ina jin sautin motarsu,” in ji shi.

A lokacin da aka wallafa labarin, ba a tabbatar da adadin asarar gaba daya ba, ko kuma ko akwai wanda ya rasa ransa.

A cewar Daily Trust, wasu masu sana’o’i a kasuwar sun nuna damuwa kan abin da suka kira jinkiri wajen amsa kira daga hukumomin agaji, suna mai cewa da an yi gaggawa, an rage girman asarar.

Wannann iftila’i dai, ya faru ne mako guda bayan da gobara ta tashi a kasuwar Singer da ta shafi ’yan kasuwa fiye da 1,000 a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here