Home Labarai Majalisar dokokin Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin gwamna

Majalisar dokokin Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin gwamna

0

Majalisar dokokin jihar Kano, ta fara shirin tsige mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, matuƙar ya gaza kare kansa bisa zarge-zargen da ta ke yi masa.

Majalisar ta fara wannan shiri ne bayan ta rubutu masa takardar sanarwa domin ya kare kansa kan zarge-zargen da ka iya kai ga tsige shi daga mukami.

A wani zama na musamman da majalisar ta gudanar a yau Alhamis, an karanta takardar sanarwar a zauren majalisar, wadda ta ƙunshi zarge-zargen aikata manyan laifuka da suka haɗa da rashin ɗa’a a aiki, yin amfani da iko ba bisa ka’ida ba da kuma karya amana ga jama’a.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husaini Chediyar Yan Gurasa, wanda ya gabatar da takardar, ya tabbatar da wannan mataki ga manema labarai bayan kammala zaman majalisar.

Ya bayyana cewa takardar sanarwar tsige mataimakin gwamnan ta samu sa hannun mambobi 38 na majalisar dokokin jihar.

A cewarsa, bayan miƙa masa takardar, ana sa ran mataimakin gwamnan zai mayar da martani ga majalisar cikin makonni biyu domin kare kansa kan zarge-zargen da ake masa.

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here