Gwamnatin Kano ta dauki nauyin kula da lafiyar wata mata mai jego mai suna Hafsatu Yusuf, wadda ta haifi ƴaƴa 5 a asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad.
Gwamnatin, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ma’aikatar lafiya Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya fitar da yammacin yau Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewa, mijin matar, mai suna Malam Salisu Nafi’u, direban babur mai kafa uku wanda aka fi sani da Adaidaita Sahu, ya bayyana jin dadinsa da wannan mataki na gwamnati, inda ya ce hakan ya zo musu a dai-dai lokacin da suke matukar bukata.
Rahotonni sun nuna cewa uwa da jariran na karbar kulawa ta musamman daga likitoci da sauran ma’aikatan lafiya domin tabbatar da lafiyarsu.
Haka kuma, sanarwar ta ce, Wannan mataki na daga cikin kokarin Gwamnatin Jihar Kano na inganta harkokin kiwon lafiya, musamman wajen kula da mata masu juna biyu da jarirai, tare da rage mace-macen mata da kananan yara.
Gwamnatin ta kuma jaddada kudurinta na ci gaba da tallafawa al’umma, musamman masu karamin karfi, domin tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya a fadin jihar Kano gaba daya.







