Wani jirgin sama mallakin kamfanin Flybird, ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano MAKIA da safiyar yau Lahadi.
Wani Video da jaridar SOLACE BASE ta wallafa a shafinta na Facebook, ya nuna yadda jirgin mai ɗauke da mutane 11, ciki har da ma’aikatan jirgin 3, ya yi hatsari da misalin karfe 9:30 na safe a kan hanyarsa ta zuwa Kano daga Abuja.
Danna Play a ƙasa domin kallon Bidiyon
A cewar wani shaida, an yi nasarar kwashe fasinjojin.








