Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai na jaridu, Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana yawaitar yin sauyin sheƙa da ƴan siyasa ke yi zuwa jam’iyyar APC da cewa, abu ne da ke nuna amincewa da shugabancin Shugaba Bola Tinubu da kuma alkibilar gwamnatinsa.
Jaridar Solacebase, ta ruwaito cewa Abdulaziz ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga taron magoya bayan APC a unguwar Fagge a birnin Kano.
Abdulaziz ya ce, salon shugabancin Shugaba Tinubu na bai wa kowa dama ya jawo mambobi daga jam’iyyu daban-daban da kuma yankuna daban-daban na ƙasar nan.
A cewarsa, babu wata jam’iyya a Najeriya da ke wakiltar haɗin kai kamar APC, inda ya nuna cewa jam’iyyar ta samu ƙarfi ta hanyar haɗa mutane daga sassa daban-daban na ƙasa.
Abdulaziz ya kuma bayyana cewa wasu gwamnonin jihohi daga yankin Kudu maso Kudu sun haɗa kai da APC, tare da nuna cewa jam’iyyar na ƙara samun karɓuwa a yankin Kudu maso Gabas, lamarin da ke nuna yiwuwar ƙarin sauya sheƙa nan gaba.
Ya yi watsi da sabuwar ƙungiyar adawa da aka kafa, inda ya nuna cewa babu wani gwamna mai ci da ke cikinta, alamar cewa ba ta da ƙarfi a halin yanzu.
A bangaren ci gaban tattalin arziƙi da ayyukan more rayuwa, Abdulaziz ya bayyana manyan shirye-shiryen tattalin arziƙi, ayyukan gina hanyoyi da layin dogo da ke gudana, biyan diyya ga al’ummomin da ayyukan gine-gine suka shafa, da kuma samar da iskar gas ta CNG a matsayin tallafin rage farashin sufuri.
Ya kawo misalin hanyar Sokoto zuwa Badagry mai layi biyu da kuma manyan ayyukan gina hanyoyi a jihohin Arewa da suka haɗa da Kano, Neja da Katsina, a matsayin hujjar yunƙurin ci gaban da gwamnatin ke aiwatarwa.
Haka kuma, Abdul’aziz Abdul’aziz, ya ƙara da cewa gyare-gyaren da shugaban ƙasa ke yi an tsara su ne domin samun kwanciyar hankali na dogon lokaci da wadatar rayuwa ga kowa.








