Home Labarai Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kaso 14.45- NBS

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kaso 14.45- NBS

0
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya na ci gaba da raguwa karo na takwas a jere a watan jiya na Nuwamba, lamarin da ya samo asali daga raguwar hauhawar farashin abinci a faɗin ƙasar.

Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, ce ta bayyana hakan ta cikin sabbin alkaluman da ta fitar, inda ta nuna cewa matsin lamba kan farashi ya ragu idan aka kwatanta da watannin da suka gabata.

Raguwar ta kai kaso 1.6 idan aka gwada da watan da ya gabata, abin da ke nuna sauƙin hauhawar farashi a tattalin arzikin ƙasar bayan dogon lokaci na tsananin hauhawar farashi.

A cewar bayanan da ta fitar a baya bayan nan, hauhawar farashin kayayyakin masarufi ta tsaya a kashi 14.45 a shekara-shekara a watan Nuwamba, sauka daga kashi 16.05 da aka samu a watan Oktoba.

Raguwar hauhawar farashin a wannan shekara ta biyo bayan shekarun da farashi ya yi tashin gwauron zabo, wanda ya jefa rayuwar jama’a cikin tsadar rayuwa a Nijeriya mai yawan al’umma.

Hukumar ƙididdigar ta Najeriya NBS, ta kuma bayyana cewa, hauhawar farashin ya kai kusan kashi 35 a watan Disamban bara, kafin ya fara raguwa bayan da aka sabunta shekarar tushe da kuma daidaita nauyin kayayyaki a ma’aunin lissafin farashi, yayin da babban bankin ƙasa CBN ya nuna burinsa na ganin hauhawar farashi ya ci gaba da raguwa.

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here