Home Labarai Shugaban NUJ na Najeriya ya yabi Ƙungiyar ta Kano tare da buɗe...

Shugaban NUJ na Najeriya ya yabi Ƙungiyar ta Kano tare da buɗe Ofishin Ƴan jaridar Internet

0

 

Shugaban na NUJ ya kuma nuna godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ƙaunarsa da aikin jarida da kuma  saka jari da yake yi a fannin aikin jarida. A cewarsa, goyon bayan gwamnan ya taimaka matuƙa wajen ƙarfafa aikin jarida a jihar.

 

Yayin da yake kiran ‘yanjarida da su rungumi ƙwarewa da alhakin aiki yayin shirin shiga shekarar 2026, Kwamared Yahaya ya bukaci mambobi da su zama jakadu na kwarai ga aikin jarida ta hanyar tsara sahihin jadawalin aiki da kare martabar aikin jarida a Najeriya.

Ya ƙara bayyana cewa shugabancin ƙasa na NUJ yana ci gaba da ƙoƙari wajen kawo sababbin tsare-tsare da suka haɗa da inganta albashi ga ‘yan jarida da ke aiki a kafafen yaɗa labarai na gwamnatin tarayya. Ya ce ana ci gaba da tattaunawa da Ministan Yaɗa Labarai, tare da nuna kyakkyawan fatan cewa idan an aiwatar da wannan mataki a matakin tarayya, ƙungiyar za ta matsa lamba a aiwatar da shi a jihohi 36 na ƙasar.

Kwamared Yahaya ya kuma bayyana shirin ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya ga ‘yan jarida, da nufin rage nauyin kuɗin magani daga aljihunsu, rage mace-macen mata masu juna biyu, da kuma tallafa wa shirin samar da inshorar lafiya ga kowa da kowa.

Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, ya jaddada kudurin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da kula da walwala da ci gaban aikin ‘yan jarida.

Ya bayyana wasu sauye-sauyen da ma’aikatar ta kawo ciki har da shirye-shiryen habaka ƙwarewar yanjarida, tsara dokar yaɗa bayanai ta jihar, haɗa ‘yanjarida na kafafen yada labarai na kowanne bangare.

Shugaban NUJ na jihar Kano, Kwamared Sulaiman Abdullahi Deideri, ya ce makon ‘yan jarida na shekarar 2025 an tsara shi ne don ƙarfafa haɗin kai da haɗin guiwa tsakanin mambobi. Ya bayyana cewa ayyukan da aka gudanar sun haɗa da addu’o’i, wasan sada zumunta, horo, da ziyartar mambobin da ke fama da rashin lafiya da iyalan waɗanda suka rasu.

An kammala taron ne da bayar da lambobin yabo ga Kwamishinan Yaɗa Labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya da tsohon Shugaban Ƙungiyar Editoci ta Najeriya Baba Halilu Dantiye da Darakta Janar na harkokin yaɗa labarai da harkokin sadarwa ga Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa.

Haka kuma a ƙarshen taron an kaddamar da ofishin ƙungiyar ƴan jarida na ƙafar Intanet watau Kano Online Media Chapel, KOMC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here