Shugaban Hukumar Kula da harkokin Man Fetur ta Najeriya, NMDPRA Farouk Ahmed, ya mika takardar murabus dinsa daga aiki.
Hakan dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan zargin cin hanci da rashawa da shugaban kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya yi masa.
Gbenga Komolafe na Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya, NUPRC shi ma ya yi murabus daga nasa mukamin.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya sanar da murabus din a wata sanarwa da ya fitar a daren yau Laraba, inda ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ne ya zabi wanda zai maye gurbin shugaban na NMDPRA.
A cewar Bayo, Tinubu ya bukaci majalisar dattijai ta amince da nadin sabbin shugabanni biyu na NMDPRA da kuma Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya, NUPRC.
“Don cike wadannan mukamai, shugaba Tinubu ya rubutawa majalisar dattawa, inda ya bukaci a gaggauta tabbatar da Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan a matsayin shugaban NUPRC da Injiniya Sa’idu Aliyu Mohammed a matsayin shugaban NMDPRA.
“Mutane biyun da aka zaba kwararrun kwararru ne a harkar mai da iskar gas,” in ji Bayo.








