Hukumar Binciken da kiyaye Hadurra ta NSIB, ta fara gudanar da bincike kan jirgin da ya yi hatsari a filin jirgin saman kasa da kasa na Sam Mbakwe da ke birnin Owerri, na jihar Imo.
Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe takwas na dare a ranar Talata, inda ya shafi jirgin sama irin Cessna 172 mallakin kamfanin Skypower Express, mai alamar rajista 5N-ASR.
Rahoton ya nuna cewa jirgin yana kan hanyarsa daga filin jirgin sama na Kaduna zuwa filin jirgin sama na Port Harcourt, kafin matuƙan jirgin su ayyana matsalar gaggawa, lamarin da ya sa aka karkatar da jirgin zuwa Owerri.
Bayan haka jirgin ya yi hatsari a yankin saukar jirage na layin sauka na 17, inda mutane huɗu ke cikin jirgin a lokacin hatsarin, kuma ba a samu asarar rai ba zuwa yanzu.
Hukumar NSIB ta bayyana cewa an sanar da ita game da hatsarin jirgin Cessna 172 mallakin Skypower Express, kuma hukumomin gaggawa na filin jirgin sama sun yi aiki cikin hanzari tare da isa wurin da lamarin ya faru ba tare da ɓata lokaci ba.
Rahoton ya ƙara da cewa ba a samu gobara bayan hatsarin ba, kuma filin jirgin saman na ci gaba da aiki yadda ya kamata, inda sauran jirage ke ci gaba da tashi lafiya bayan faruwar lamarin.








