Home Nishaɗi EFCC ta cafke jarumar Kannywood Samha Inuwa bisa zargin goge Majina da...

EFCC ta cafke jarumar Kannywood Samha Inuwa bisa zargin goge Majina da kuɗi

0

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma laifuka masu alƙa da kuɗi ta EFCC, ta kama fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood, Samha Inuwa, bisa zargin wulakanta takardar Naira.

Ofishin hukumar ta EFCC shiyyar Kano ne ya bayyana cafke jarumar, ya na mai cewa an kama Samha Inuwa ne biyo bayan wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, inda aka ganta ta na goge majina daga hancinta da takardun kuɗi ta Naira.

Ya ce, bayan yaɗuwar bidiyon, hukumar ta fara ɗaukar mataki ta hanyar gano inda take tare da kama ta domin amsa tambayoyi dangane da lamarin.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a halin yanzu ana tsare da ita a hukumar EFCC yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Hukumar ta bayyana cewa da zarar ta kammala binciken, za a gurfanar da jarumar a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here