Home Labarai Ganduje ya janye niyyarsa ta kafa sabuwar ƙungiyar Hisbah

Ganduje ya janye niyyarsa ta kafa sabuwar ƙungiyar Hisbah

0

Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da soke niyyarsa ta kafa ƙungiyar Hisbah mai zaman kanta da aka yi wa laƙanci da Hisbah Fisabilillahi a jihar Kano.

Babban Daraktan Cibiyar Ƙara Ingancin Aiki ta Najeriya kuma jigo a jam’iyyar APC a jihar Kano Baffa Babba Dan Agundi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Sanarwar ta bayyana cewa an yanke matakin ne bayan tattaunawa mai zurfi.

Haka kuma, Sanarwar ta ƙara da cewa an cimma matsayar ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya haɗa wakilai daga ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, wanda aka gudanar a ofishin kamfen na Tinubu a jihar.

Ta kuma bayyana cewa matakin janyewa daga shirin ya biyo bayan ra’ayoyi da damuwa masu yawa da jama’a suka nuna game da shirin kafa ƙungiyar Hisbah mai zaman kanta a jihar.

Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa manyan masu ruwa da tsaki sun shiga tsakani domin hana rikici da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali, ciki har da gwamnatin jihar Kano, Hukumar Tsaro ta DSS da kuma Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A cewar sanarwar, an yanke shawarar dakatar da shirin ne domin bai wa gwamnatin jihar Kano damar duba batun sallamar wasu jami’an Hisbah tare da magance matsalar ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.

Sanarwar ta jaddada girmamawa ga Hukumar Hisbah da aka kafa bisa doka a jihar Kano, tare da bayyana aniyar ci gaba da goyon bayan hukumomin tsaro na halal domin tabbatar da doka da oda da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar Kano da ƙasar baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here