Home Labarai Gwamnatin Kano ta haramta kafa ƙungiyar Hisbah tare da yin umarnin cafke...

Gwamnatin Kano ta haramta kafa ƙungiyar Hisbah tare da yin umarnin cafke mambobinta

0

Gwamnatin jihar Kano ta bayar  da umarnin haramta kafa ƙungiyar Hisbah mai zaman kanta mai laƙabin Hisbah Fisabilillahi, tare da bayyana ayyukanta a matsayin haramtattu kuma barazana ga zaman lafiya da tsari a jihar.

Umarnin, wanda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu, ya nuna cewa gwamnati ta gano ana ci gaba da ɗaukar matasa, horas da su da kuma tattara su cikin ƙungiyar ba tare da sahalewar doka ba, lamarin da ya saba wa dokar Hukumar Hisbah ta jihar Kano.

Da ya ke sanar da wannan umarni, Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa Hukumar Hisbah ita kaɗai ce hukuma da doka ta amince da ita wajen tsarawa da gudanar da dukkan ayyukan Hisbah a faɗin jihar.

Gwamnatin ta ƙara da cewa bayyanar wannan ƙungiya ta daban na nufin kafa wata rundunar tilasta doka ba tare da izini ba, abin da zai iya lalata zaman lafiyar al’umma tare da tauye ikon da doka ta bai wa Hukumar Hisbah.

Umarnin zartarwar ya tanadi cewa ba ya halatta ga kowane mutum ko ƙungiya su ɗauki mutane, su tara su, su horas da su ko su tura su domin gudanar da wata Hisbah ta daban ko wata rundunar tilasta doka makamanciyarta a cikin jihar Kano.

Haka kuma, gwamnan ya ayyana dukkan ayyukan ƙungiyar a matsayin haramtattu, ba bisa doka ba kuma marasa inganci, tare da gargadin cewa duk wanda ya yi koyi da kayan aiki, alamomi ko ikon Hukumar Hisbah zai fuskanci hukunci bisa doka.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umurci Rundunar ƴan sandan Najeriya, Hukumar tsaron farin kaya ta DSS, Hukumar tsaro ta Civil Depence da sauran hukumomin tsaro da su binciki masu jagorantar ƙungiyar, su dakatar da duk wani ɗaukar mambobi ko horaswa da ake yi, sannan su ɗauki matakan doka da suka dace domin hana rushewar doka da oda.

Haka kuma, gwamnatin ta an ƙarar da jama’a cewa shiga, tallafawa ko alaƙantuwa da ƙungiyar da aka haramta laifi ne a ƙarƙashin dokokin jihar, yayin da aka shawarci mutanen da aka riga aka ɗauka su janye daga ƙungiyar tare da kai rahoto ga cibiyar tsaro mafi kusa, ofishin Hisbah ko ofishin ƙaramar hukuma.

Umarnin ya tanadi hukunci ga masu karya doka ciki har da gurfanarwa kan taron ba bisa ka’ida ba, kwaikwayon hukuma da kuma kafa rundunar tsaro ba tare da izini ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here