Home Labarai Matatar Dangote ta rage farashin litar Fetur zuwa Naira 699

Matatar Dangote ta rage farashin litar Fetur zuwa Naira 699

0

Majiyoyi daga matatar  sun tabbatar da sabon farashin a ranar Alhamis, inda suka ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na sa farashin fetur na cikin gida ya kasance mai sauki a kasuwa.

Shugaban kungiyar dillalan man fetur na ƙasa masu zaman kan su IPMAN, Abubakar Garima, ya tabbatar da ci gaban, inda ya ce, matatar ta bai wa masu sayarwa shawarar fara ɗaukar fetur a sabon farashin domin shirin bukukuwan ƙarshen shekara.

Raguwar farashin ta kawo farashin fetur kusa da matakin da aka samu shekaru biyu da suka wuce, inda wannan ya kasance ɗaya daga cikin mafi girman raguwar farashi tun lokacin da matatar ta fara samar da fetur a cikin gida.

Shugaban rukunin kamfanin Aliko Ɗangote, ya yi alkawarin cewa matatar za ta ci gaba da rage farashin domin ta kasance mai sauki idan aka kwatanta da fetur da ake shigowa da shi daga waje.

Ya ce farashin fetur da dizel za su ci gaba da kasancewa a kasuwa a farashi mai sauƙi sosai.

Raguwar farashin Ɗangote ya biyo bayan irin wannan mataki da NNPCL ta ɗauka, wanda a ranar 27 ga Nuwamba ta rage farashin fetur a tashoshin sayarwa zuwa Naira 900 a lita a Legas da Naira 940 a lita a Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here