Kwamitin gwamnatin Kano mai aikin tsaftace tashoshin mota da kasuwanni wuraren taruwar jama’a da kuma yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ya ƙwato tarin miyagun ƙwayoyi da gurɓattu har ma da na Jabu a kasuwar sayar da magunguna ta Kano da ke yanki Ɗan-Gwauro a ƙaramar hukumar Kumbotso a nan Kano.
Kwamitin ya yi wannan aiki ne a dare Talatar makon nan yayin da ya kai ziyara kasuwar bayan da shugaban kasuwar ya sanar da gwamnatin Kano cewar za su bai wa gwamanati ƙwayoyin domin ta lalata su.
Kwamitin ya balle wani dakin ajiyar kayayyaki da ke ofishin shugaban kasuwar ne, inda ya same shi makare da wasu miyagun kwayoyi na fiye da Naira biliyan 1.
Tun da farko shugaban kasuwar Alhaji Husaini Labaran Zakari, ƴa ki amincewa ya bude dakin da suka adana miyagun kwayoyin ne bayan da ya bayar da wasu masu tarin yawa da suka hadar da wadanda wa’adin amfaninsu ya ƙare da na Jabu waɗanda kuɗinsu ya haura naira biliyan ɗaya da miliyan dari biyar.
Ya ce, “wasu daga cikin magungunan da suka bai wa gwamnatin sun ƙwato su ne yayin da wasu kuma daga ciki masu su ne suka kai musu su domin raɗin kansu.”
“Wadannan magunguna kuka gani ana yin bincike ne a kansu, har jami’an hukumar NDLEA sun san da su, kuma akwai Katan ɗaya ma da ni da kaina na ɗauka na kai wa Sakataren gwamnatin Kano tare da shaida masa irin kokarin da muke yi na yaki da sayar da irin wadannan magunguna, har yanzu haka Katan ɗayan ma ya na hannu Sakataren gwamnati, a cewar Husaini Labaran Zakari.”
ƴa kuma ce, ba mu da wata matsala tsakaninmu da gwamnati, hasali ma sai irin haɗin kai da muke bayarwa na ganin an tsaftace jihar Kano daga masu shigo da miyagun kwayoyi suna lalata rayuwar matasan mu.”
Da ya ke jawabi bayan karbar magungunan, shugaban kwamitin Manjo Adamu Abubakar Usman mai ritaya, ya bayyana cewa, sun karbi kayan wadanda aka cika babbar motar dakon kaya watau Trailer, Inda za su miƙa su ga gwamnatin jihar Kano, domin ta ɗauki matakin da ya dace a kansu.
“Gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta ƙirƙiro wannan kwamiti ne domin ganin ta kawo gyara musamman ma a fannin yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar Kano, in ji Manjo A.A Usman Mai ritaya.
Ya ƙara da cewa, Akwai bayanan sirri da muka samu na cewa akwai wadannan miyagun ƙwayoyi, sannan akwai wadanda kuma shugabannin kasuwar ne da kansu suka sanar da mu cewar sun kama kayan tare da kuma da wasu da masu su suka kai musu.
Shugaban kwamitin, ya kuma bukaci dukkan yan kasuwar da su riƙa basu bayanai na sirri domin taimaka musu wajen yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar Kano.








