Shugaban kasa Bola Tinubu ya zaɓi Ambasada Ismail Abba Yusuf, a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga, ya fitar da yammacin yau Laraba.
Sanarwar ta ruwaito cewa, shugaba Tinubu ya aike da wasika zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, inda ya bukaci da ta tantance tare da tabbatar da Ambasada Ismail Abba Yusuf domin maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a farkon makon nan.
Ambasada Ismail Abba Yusuf dai, gogaggen jami’in harkokin diflomasiyya ne wanda ya taɓa zama jakadan Najeriya na musamman kuma mai cikakken iko a ƙasar Turkiyya daga shekarar 2021 zuwa 2024.








