Home Labarai Rwanda ta musanta hannun a sabon rikicin da ya ɓarke a Kivu...

Rwanda ta musanta hannun a sabon rikicin da ya ɓarke a Kivu ta DR Congo

0

Ƙasar Rwanda ta musanta cewa ba ita ke haddasa sabbin rikice-rikicen da ya kunno kai a Kivu ta Kudu da ke DR Congo.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da ma’aikatar harkokin wajen Rwanda ta fitar.

Rwanda ta kuma zargi rundunar DRC da ta Burundi, tare da mayakan FDLR da Wazalendo da wasu ‘yan kasashen waje da kai hare-hare da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan ƙauyuka kusa da kan iyakar Rwanda.

Rwanda ta ce hakan ya tilasta wa sama da ‘yan Congo 1,000 tserewa zuwa ƙasar, inda aka basu masauki a Bugarama.

Haka kuma, Rwanda ta ce Burundi ta tura sojoji 20,000 a Kivu ta Kudu domin yi wa al’ummar Banyamulenge a Minembwe ƙawanya.

Rwanda ta yi gargadi cewa irin waɗannan matakai na kawo barazana ga zaman lafiya a yankin, tana mai kira a koma ga yarjejeniyar da Amurka ke mara wa baya da kuma kammala sauran sashe na yarjejeniyar Doha tsakanin DRC da M23/AFC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here