Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin badi na fiye da naira tiriliyan 58 da biliyan 18 a gaban zaman haɗin gwiwa na Majalisun tarayya.
Kasafin, wanda aka sanya masa taken kasafin ƙarfafa nasarori, sabunta juriya da bunƙasa ci gaban bai ɗaya, ya mayar da hankali ne kan inganta nasarorin tattalin arziƙi da aka samu, dawo da amincewar masu zuba jari da sauya farfaɗowar tattalin arziƙi zuwa ayyukan yi da ingantaccen rayuwa ga ‘yan ƙasa.
A jawabin da ya gabatar, shugaban ƙasa ya bayyana cewa dukkan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke aiki ba tare da izinin gwamnati ba, wanda ake ɗauke su a matsayin ‘yan ta’adda.
Ya kuma jaddada ƙudurin ɗaukar tsauraran matakan tsaro, ƙarfafa daidaito wajen aiwatar da kasafi da zurfafa sauye-sauyen tattalin arziƙi domin tinkarar matsalolin tsaro da bunƙasa zaman lafiya.
Shugaban ƙasa ya bayyana cewa tattalin arziƙin ƙasar na nuna alamun daidaituwa, inda ya ambaci haɓakar tattalin arziƙi da aka samu, raguwa a hauhawar farashi na tsawon watanni da dama, ƙaruwa a samar da man fetur, ingantaccen samun kuɗaɗen shiga daga sassan da ba na mai ba, da kuma ƙaruwa a amincewar masu zuba jari.
Ya kuma bayyana cewa ajiyar kuɗaɗen waje ta kai matakin da ba a samu irin sa ba cikin shekaru da dama, lamarin da ke ƙarfafa ikon ƙasar wajen shigo da kayayyaki.
A tsarin kuɗaɗen kasafin, an kiyasta jimillar kuɗaɗen shiga da za a samu da Naira Tiriliyan 34.33, yayin da jimillar kashe kuɗaɗe ta kai Naira Tiriliyan 58.18, ciki har da kuɗaɗen biyan basussuka.
An ware kuɗaɗe masu yawa ga ayyukan raya ƙasa, ilimi, lafiya da tsaro, inda bangaren tsaro ya samu kaso mafi tsoka domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da aikata laifuka.
Kasafin ya kuma gindaya hasashen farashin danyen mai, yawan man da za a rika hakowa a kullum, da kuma farashin musayar kuɗaɗe.
Shugaban ƙasa ya jaddada cewa waɗannan alkaluma suna nuna fifikon ƙasa wajen tabbatar da dorewar kuɗaɗe, bayyananniyar biyan basussuka da kashe kuɗaɗe bisa ƙima.
Dangane da aiwatar da kasafi, shugaban ƙasa ya amince cewa aiwatar da kasafin da ya gabata ya fuskanci ƙalubale, amma ya bayar da umarnin tsaurara bin ƙa’idoji a shekarar 2026.
Ya umarci hukumomin kuɗi da kasafi da su aiwatar da kasafin bisa cikakkun bayanai da jadawalin da aka amince da su, tare da tilasta wa hukumomin gwamnati cika wajibcin samun kuɗaɗen shiga.
Shugaban ƙasa ya jaddada cewa muhimmancin kasafi ba wai sanarwa ba ce kaɗai, illa aiwatarwa, kuma kasafin na shekarar 2026 na nufin amfanin kowa da kowa, tare da nuna ƙwarin gwiwar cewa haɗin gwiwar ɓangaren zartarwa da na majalisa zai tabbatar da cimma muradun shirin sabuwar fata ga ƙasa.
Solacebase








