Home Labarai Motoci fiye da 1,000 na ɗaukar fetur kullum a matatar Dangote bisa...

Motoci fiye da 1,000 na ɗaukar fetur kullum a matatar Dangote bisa Ragin farashi

0

Matatar mai ta Dangote ta bayyana cewa a halin yanzu motoci sama da 1,000 na ɗaukar fetur kullum daga matatar.

Wannan lamarin ya nuna yadda matatar ta zama cibiyar rarraba mai a faɗin Najeriya bayan wasu muhimman gyare-gyare da aka aiwatar domin sauƙaƙa samun makamashi.

Wata sanarwar da aka fitar ta nuna cewa wannan ci gaban ya biyo bayan rage farashin famfo na man fetur zuwa naira 699 kan kowace lita, tare da rage mafi ƙarancin adadin saye daga lita miliyan biyu zuwa lita dubu 250, matakan da suka ƙarfafa wadata da kuma buɗe ƙofofi ga ƙanana da manyan ‘yan kasuwa.

Matatar ta ƙara da cewa an bullo da tsarin tabbacin banki na kwanaki 10 domin tabbatar da ci gaba da isar da mai ba tare da tsaiko ba, tare da ƙara amincewar ‘yan kasuwa da ayyukan matatar a ɓangaren kasuwancin man fetur na ƙasa.

Bayan rage farashin, an samu karuwar cunkoso daga ‘yan kasuwar mai, inda a yanzu ake ganin motoci sama da 1,000 na ɗaukar man fetur kullum daga tashar lodin matatar, alamar yadda kasuwa ke amincewa da inganci da jagorancin matatar Dangote a ɓangaren ƙasa-ƙasa na man fetur.

Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya jaddada cewa manufar kamfanin ita ce sauƙaƙa farashi da wadatar makamashi ga kowane ɗan Najeriya, tare da bai wa manya da ƙananan ‘yan kasuwa damar shiga kasuwa domin tabbatar da isar da mai zuwa kowane lungu na ƙasa.

Matatar ta ƙara da cewa, wannan tsari yana ƙarfafa hanyoyin rarrabawa, yana buɗe kasuwa ga ƙanana, tare da inganta wadatar man fetur a ƙasa baki ɗaya, yayin da ƙungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu ta ƙarfafa mambobinta su yi ciniki da matatar Dangote, tana mai nuni da cewa farashinta shi ne mafi sauƙi a halin yanzu, kuma ana sa ran fara isar da mai kyauta a watan Janairu 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here