Home Labarai Tinubu ya sauka a Bauchi don yin ta’aziyyar Sheikh Dahiru Usman 

Tinubu ya sauka a Bauchi don yin ta’aziyyar Sheikh Dahiru Usman 

0

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauka a jihar Bauchi yau Asabar domin yi ta’aziyya ga gwamnatin jihar da kuma iyalan shahararren malamin addinin Musulunci marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Sheikh Dahiru Bauchi, wanda shi ne jagoran darikar Tijjaniyya a Najeriya, ya rasu ne a ranar 27 ga Nuwamba, lamarin da ya jawo alhini a faɗin ƙasar saboda rawar da ya taka a addini da tarbiyyar al’umma.

Tinubu ya sauka a filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe huɗu da mintuna goma na yamma, inda rundunar sojin saman Najeriya ta tarbe shi da gaisuwar faretin girmamawa.

Shugaban ƙasar ya samu rakiyar gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, ɗansa Seyi Tinubu, da wasu manyan jami’ai, yayin da gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang, Ministan lafiya na haɗin gwiwa Farfesa Muhammad Ali Pate, Ministan harkokin wajen ƙasa Yusuf Tuggar, da Sanata Shehu Buba na APC daga Bauchi ta Kudu suka tarbe shi.

Bayan ziyarar jaje, ana sa ran Tinubu zai wuce jihar Legas domin shafe hutun ƙarshen shekara, yayin da ake ci gaba da karɓar ta’aziyya daga sassa daban-daban na ƙasar.

Sheikh Dahiru Bauchi, mai shekaru 98, ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda aka yi masa jana’iza bisa koyarwar Musulunci, kuma an san shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan malamai masu tasiri a Najeriya, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa ilimin addini, zaman lafiya, haɗin kai, tarbiyyar matasa da jagoranci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here