Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da Kudirin Kasafin Kuɗin baɗi a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar Jumma’a, 19 ga Disamba, 2025.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin maga takardar majalisar ya fitar aka raba ga mambobin majalisar.
Kafin gabatarwar, ana sa ran Majalisar Wakilai za ta karanta wasiƙar sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa a zaman majalisa na yau Al’hamis
Wasiƙar ta fayyace tsauraran matakan tsaro da shiga harabar Majalisar, inda aka umarci duk masu ruwa da tsaki su kasance a wuraren aikinsu kafin karfe 11:00 na safe.
Bayan wannan lokaci, za a takaita shiga Majalisar, yayin da aka gargadi waɗanda ba su da izini su nisanci harabar, domin gabatarwar kasafin kuɗi ita ce matakin farko na mika shirin kuɗin gwamnati ga majalisa.








