Home Siyasa Siyasar Kano na ci gaba da ɗaukar ɗumi

Siyasar Kano na ci gaba da ɗaukar ɗumi

0

Yayin da, ake raɗe-raɗin cewa, gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheƙa daga, jam’iyyar NNPP zuwa babbar jam’iyyar adawa a Kano ta APC, harkokin siyasa na Siyasa ci gaba da ɗaukar ɗumi.

Zuwa yanzu dai a iya cewa kawuna ƴaƴan jam’iyyar na neman rabuwar gida biyu, watau ɓangaren masu goyon bayan ficewar gwamnan da kuma waɗanda basa goyon bayan saying sheƙar.

A Litinin ɗin makonnan yayin taron manema labarai, shugaban jam’iyyar NNPP na Kano Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya roƙi mambobinta da su yi wa Allah da ma’aiki kada su koma APC.

Sai dai sa’o’i kaɗan bayan wannan roƙon ne shugabannnin mazaɓarsa ta Gargari a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, suka yi wani taro tare da sanar da cewa sun kore shi daga jam’iyyar ta NNPP bisa zarginsa da rarraba kawunan mabiyanta.

Ana haka kuma sai ga ɓullar hotunan mataimakin gwamnan Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo da shugaban ma’aikatar Kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire ta jihar Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata a matsayin ƴan takarar Gwamna da mataimaki a zaɓe mai zuwa.

Lamarin da ke nuni da cewa kenan ko da gwamna Abba Kabir ya sauya sheƙa su ne za su maye gurbinsa wajen yi wa jam’iyyar takara a zaɓen da ke tafe ma shekarar 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here