An fara sayar da wannnan na’urar wankan Dan-adam ta zamani da ta yi kamanceceniya da na’urar wankin kaya inda yanzu haka ta shiga kasuwa a kasar Japan bayan da ta ja hankalin dubban baƙi a taron bajakolin duniya wanda aka yi wa lakabi da World Expo Osaka da ya gudana a watan Oktoba, inda fiye da mutane miliyan 27 da suka halarci taron suka nuna sha’awarsu ga na’urar.
Na’urar, wadda wani kamfani na kasar Japan ya kirkira, a cewar mai magana da yawun kamfanin a baya-bayannan, mai bukatar wanka zai shiga cikinta ne ya yi kwanciyarsa inda ita kuma za ta cuda shi ciki da bai ba tare da jujjuyawa ba kamar injin wanki ba.
A cewar Kamfanin da ya ƙera wannan na’ura, ba wanka kawai ya ke yi wa mutane ba, injin ya na kuma sanya ido kan bugun zuciya da lafiyar wanda ya ke cuɗawa.
Haka kunm, kamfanin ya ce, ya fara nazarin samar da wannan fasaha ne tun a shekarar 1970, tun Shugaban kamfanin ya na yaro.
Wani otal a Osaka ne ya fara kafa tarihin sayen na’urar ta farko domin bai wa baƙinsa tukwicin sulluɓe su suɓul, yayin da wasu kamfanoni ke fatan amfani da ita don jan hankalin kwastomomi.
Kamfanin ya ce za a ƙera kimanin injinan guda 50 kacal, kuma farashin duk 1 ya kai yen miliyan 60, kusan dala dubu 385 wanda ya yi dai-dai da Naira miliyan ɗari biyar da talatin da tara.







