Home Tsaro Kaduna: Ƴan sanda sun tabbatar da sace ƙwararren ɗan jarida

Kaduna: Ƴan sanda sun tabbatar da sace ƙwararren ɗan jarida

0

Rundunar ƴan sanda jihar Kaduna, ta tabbatar da sace wani ƙwararren ɗan jarida mai ɗaukar hoto, Malam Umar Usman a cikin jihar Kaduna, lamarin da ya jefa al’umma da ’yan uwansa cikin damuwa.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Mansir Hassan, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a yau Talata.

Ya ce, rundunar ta ƙaddamar da bincike domin gano inda aka kai Malam Umar Usman cikin koshin lafiya ba tare da wani lahani ba.

Haka kuma, ya ƙara da cewa, an sace ɗan jaridar ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren jiya Litinin, a unguwar Danhonu II da ke Millennium City, a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, daga gidansa, wanda tsohon ma’aikaci ne a gidan talabijin na AIT reshen Kaduna, sannan kuma ya taɓa yin aiki a Hukumar Talabijin ta Ƙasa NTA reshen Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa kwamishinan ’yan sanda na jihar Kaduna, Malam Rabiu Muhammad, ya gaggauta tura tawagar jami’ai domin bin sawun masu garkuwa da mutane tare da tabbatar da an ceto Malam Umar Usman cikin koshin lafiya.

Rundunar ’yan sandan ta kuma yi kira ga al’ummar yankin da su bayar da duk wani sahihin bayani da zai taimaka wajen gano inda aka kai ɗan jaridar da kuma ceto shi cikin gaggawa.

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here