Home Siyasa Da ɗumi-ɗumi: Majalisar dokokin Rivers na shirin tsige gwamna Fubara

Da ɗumi-ɗumi: Majalisar dokokin Rivers na shirin tsige gwamna Fubara

0

Mambobin Majalisar Dokokin Jihar Ribas sun fara daukan matakan tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu bisa zarginsu da aikata manyan laifuffuka.

A zaman majalisar na yau Alhamis karkashin jagorancin shugaban Majalisar Martins Amewule, shugaban masu rinjaye Major Jack ya karanta sanarwar zarge-zarge da manyan laifuffuka da aka jingina wa gwamnan.

Majalisar ta jingina matakin da ta ɗauka da sashe na 188 na kundin tsarin mulkin kasar nan inda Major Jack ya lissafa maki bakwai na abin da aka bayyana a matsayin manyan laifuffukan da ake zargin Gwamna Fubara da aikatawa.

Daga cikin zarge-zargen da aka ambata akwai rusa ginin majalisar dokokin da kashe kuɗaɗe ba tare da tanadin kasafin kuɗi ba, hana kuɗaɗen da suka kamata a bai wa Hukumar Hidimar Majalisar Dokoki, da kuma ƙin bin hukuncin Kotun Koli kan ’yancin kuɗin majalisar.

Sai dai zuwa lokacin fitar wannan rahoto, mambobi 26 na Majalisar Dokokin Jihar ta Rivers ne suka sanya hannu a takardar sanarwar zargin da aka gabatar, kuma shugaban majalisar ya ce, za a isar da sanarwar ga gwamnan cikin kwanaki bakwai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here