Jaridar PlatinumPost, ta ruwaito cewa, an ɗaga ranar da Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, zai fice daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa jam’iyyar APC.
A cewar jaridar, Majiyoyin da ke kusa da gwamnan sun bayyana cewa ranar da aka tsara tun da farko gwamnan zai sauya sheƙa ita ce wa domin sauyin sheƙar Litinin, 5 ga watan nan da muke ciki na Janairun shekarar 2026, amma yanzu an sauya ranar zuwa Litinin, 12 ga Janairu.
A baya, jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa Gwamna Yusuf zai sauya sheƙa zuwa APC a ranar 5 ga Janairu.
Sai dai wata majiya mai tushe, wadda ta nemi a sakaya sunanta kuma ta halarci wani taro tsakanin Gwamna Yusuf da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a Abuja ranar Juma’a, ta bayyana cewa gwamnan ya nemi ƙarin lokaci.
A cewar majiyar, gwamna Abba Kabir Yusuf, na son ci gaba da tuntubar wasu ‘yan majalisar dokokin jihar da sauran manyan masu ruwa da tsaki da har yanzu ba su bayyana cikakken goyon bayansu ga wannan yunƙurin siyasa ba.








