Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi Alla-wadai bisa kai harin kunar bakin wake a wani masallaci a kasuwar Gamboru da ke tsakiyar birnin Maiduguri, wanda ya yi sanadin rasuwar mutane biyar tare da jikkata ƙarin wasu 35.
Sanarwar da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya, ya fitar ta ruwaito cewa ana zargin wani ɗan kunar bakin wake ne cikin masallacin a daidai lokacin da ake yin sallar Magariba a jiya Laraba.
Gwamna Babagana Umara Zulum, ya bayyana lamarin a matsayin mummunan aiki na rashin imani da tauye alfarmar addini da rayuwar bil’adama.








