Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini da kaduwa bisa rasuwar ’yan Majalisar Dokokin Jihar su biyu a rana guda.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sunusi Bature dasakin Tofa ya fitar, inda ta cikinta, Gwamnan ya ce mutuwar Alhaji Sarki Aliyu Daneji mai wakiltar karamar hukumar birni da kuma Aminu Sa’adu mai wakiltar Ungoggo, ta kasance lamari mai tada hankali da taba zuciya a tarihin jihar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce, rasuwar ’yan majalisar biyu cikin kankanin lokaci kuma a rana guda ta jefa gwamnati da al’ummar Kano cikin jimami, tare da bayyana marigayan a matsayin jajirtattun masu hidima ga jama’a kuma masu gaskiya da riƙon amana, tare da jaddada cewa sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen wakiltar al’ummominsu da aikin dokoki a Majalisar Jiha.
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, Majalisar Dokokin Jihar Kano da kuma al’ummomin Kano Municipal da Ungoggo. Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta musu, Ya sanya su a Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansu da daukacin al’ummar Kano juriyar wannan babban rashi.
Tun a daren jiya Laraba ne dai gwamnan da kusoshin gwamnatinsa har ma da jagoran darikar kwankwasiyya Injinya Rabi’u Musa kwankwaso suka jagoranci yin jana’aira Aminu Sa’adu Ungogi, yayin da kuma da safiyar yau suka jagoranci jana’izar Sarki Aliyu Daneji.








