Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce Gwamnatin Tarayya ta tura ƙarin rundunonin tsaro na musamman zuwa birnin Maiduguri, domin domin bincike tare da cafke bata garin da suka kai harin bam a kasuwar Gamboru.
Kashim Shettima ya bayyana harin a matsayin mummunan ta’adanci kan fararen hula da zaman lafiyar ƙasa, ya na mai cewa, Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin ƙara tsaurara matakan tsaro a Jihar Borno.
Haka kuma, ya kara da cewa, Gwamnatin Tarayya na yin aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro na cikin gida, domin kare al’umma, inda kuma ya yi Allah-wadai da harin da ya auku a wani masallaci, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu 35.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya tabbatar da cewa jami’an tsaro ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an gurfanar da masu laifin gaban shari’a.
Ya kuma jajanta wa gwamnatin Borno, mazauna jihar da iyalan waɗanda harin ya rutsa da su, yana mai jaddada cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da bai wa hukumomin tsaro dukkan goyon bayan da ake bukata domin murƙushe ta’addanci a kowane iri.








