Gwamnatin Amurka ta sanar da kai wani mummunan hari na soji ta sama kan wuraren da ake zargin cewa maɓoyar ƴan ƙungiyar masu iƙirarin jahadi ne ta ISIS ke amfani da su a Arewa maso Yammacin Nijeriya.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ya ce an kai hare-haren ne domin dakile ayyukan ta’addanci da kashe-kashen fararen hula.
Harin ya zo ne kusan wata guda bayan Donald Trump ya yi barazanar kai farmaki kan Nijeriya, bisa zargin barin ’yan ta’adda suna kai hare-hare kan Kiristoci.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na, sada zumunta dangane da kai harin, shugaba Donald Trump, ya ce, ba zai zuba ido ba a riƙa kai hare-hare kan fararen hula musamman ma Kiristoci, don haka akwai ma wasu atisayen harin ga ƴan ta’adda a nan gaba.
Bayan sanarwar, Sakataren Yaƙin Amurka, Pete Hegseth, ya bayyana jin daɗinsa da haɗin gwiwar da Gwamnatin Nijeriya ta bayar, yana mai cewa hare-haren na daga cikin matakan kawo ƙarshen kashe-kashen fararen hula da raunana ƙungiyoyin ’yan ta’adda.








