Home Tsaro Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kai harin Amurka kan ƙungiyar ISIS

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kai harin Amurka kan ƙungiyar ISIS

0

Gwamnatin Najeriya, ta tabbatar da cewa ƙasar ta kai hari ta sama kan mambobin ƙungiyar ta’addanci ta ISIS, ta na mai cewa, ta na da haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, domin yaƙi da ta’addanci.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatarsa, Kimiebi Ebienfa, ya fitar da tsakar daren wayewar yau Juma’a.

Sanarwar ta ce kai hare-haren sun samo asali ne daga haɗin gwiwar bayanan sirri da tsare-tsaren dabaru da ake yi da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, tare da mutunta ikon ƙasar Najeriya da dokokin ƙasa da ƙasa.

Gwamnatin ta jaddada cewa kare rayukan fararen hula shi ne ginshiƙin duk wani mataki na yaƙi da ta’addanci, tare da tabbatar da cewa duk wani tashin hankali, ko da a kan Kiristoci ko Musulmi, abin Allah-wadai ne.

Haka kuma ta ce Najeriya za ta ci gaba da aiki da abokan hulɗa domin raunana ƙungiyoyin ta’adda, katse hanyoyin kuɗaɗensu da dabarunsu, da kuma ƙarfafa tsaron ƙasa da na bayanan sirri, tare da sanar da jama’a ta hanyoyin hukuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here