Hukumomin kasar Ghana sun kori ƴan Najeriya 42 daga yankin Ashanti bayan kotu ta same su da laifukan da suka shafi karuwanci, da damfara da wasu laifuka daban-daban.
Ministan Yankin Ashanti, Frank Amoakohene, ne ya bayyana hakan ta shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 18 ga Disamba, 2025, kamar yadda NewsPoint Nigeria ta ruwaito.
A cewarsa, ba ƴan Nijeriya kaɗai aka kora ba, an kuma kori ƴan ƙasashen Kamaru 13, da Ivory Coast uku, da Burkina Faso uku, da Benin bakwai, lamarin da ya kai adadin waɗanda aka kora zuwa mutum 68 baki ɗaya. Ya ce matakin ya biyo bayan hukuncin kotuna ne kan laifukan da suka shafi Q-Net, karuwanci da sauran aiyukan laifi.
Amoakohene ya yabawa Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ghana bisa jajircewarta wajen aiwatar da dokokin ƙasa cikin gaskiya, tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam. Ya ce haɗin gwuiwar hukumar da kotuna da sauran jami’an tsaro na taimakawa wajen kare jama’a da tabbatar da doka da oda a yankin.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara sanya ido kan ƴn Nijeriya a ƙasashen waje, inda wasu ƙasashe ke ba da rahoton kama ƴan ƙasa da ake zargi da aikata laifukan ƙungiyoyin aikata laifuka da karya dokokin shige da fice. A wani lamari makamancin haka, hukumomin Indiya sun kama ƴan Nijeriya fiye da 50 a ƙarshen Nuwamba, bisa zargin hannu a harkokin fataucin miyagun ƙwayoyi da safarar kuɗi a manyan biranen ƙasar.








