Home Tsaro Kotu ta yanke wa Dagaci hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu ta yanke wa Dagaci hukuncin kisa ta hanyar rataya

0

Wata Babbar Kotu a Jihar Gombe, ta yanke wa Dagacin Gundumar Bangunji, Sulei Yerima, da Shedrack Aliyu hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun su da laifin aikata kisan kai.

Kotun mai lamba 8 da ke zamanta a Gombe, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Abdulsalam Mohammad, ta ce an same su da laifi ne bayan an tabbatar da tuhumar da ake yi musu.

A hukuncin da ya yanke, alƙalin kotun ya kuma wanke tare da sallamar wasu mutum uku sakamakon rashin isassun hujjoji a kansu.

Tun da farko, an gurfanar da mutanen a gaban kotu ne, bisa laifukan haɗa baki, tayar da hankali, jikkata mutum, da kisan kai.
A ƙarshe, kotun ta yanke wa Dagacin Bangunji, Sulei Yerima, da Shedrack Aliyu Kwan hukuncin kisa ta hanyar rataya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here