Home Tsaro Rundunar Sojin sama ta biya diyya ga mutanen da harin dakarunta ya...

Rundunar Sojin sama ta biya diyya ga mutanen da harin dakarunta ya shafa a Sokoto

0

Rundunar sojin saman Najeriya, ta biya diyya ga mutanen da harin sojin sama bisa kuskure ya shafa da kuma iyalan waɗanda suka rasu a jihar Sokoto.

Harin dai, ya shafi mutanen yankunan Gidan Bisa da Rumtuwa da ke ƙaramar hukumar Silame, inda aka samu asarar rayuka da jikkata.

Rundunar ta bayyana rahoton biyan diyyar ne ta cikin wata sanarwa da Daraktanta na hulɗa da jama’a da yada bayanai Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar yau Lahadi a Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewa, an dauki matakin biyan diyya ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin tausaya wa jama’a da kuma gyara abin da ya faru.

Haka kuma, rundunar ta bayyana cewa ta na daraja dangantakarta da al’ummomi tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin sojoji da fararen hula.

Haka kuma ta cikin sanarwar, Babban hafsan sojojin saman Najeriya ya yaba da rawar da gwamnatin jihar Sokoto ke takawa wajen ƙarfafa tsaro da haɗin kan jama’a, musamman ta hanyar manufofin tsaro da aka samar a matakin jiha.

Ya nuna cewa irin waɗannan matakai na cikin gida suna taimakawa ayyukan tsaro na tarayya wajen rage ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan fashi.

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here