Home Tsaro Ƴan sanda sun cafke waɗanda suka shirya yin garkuwa ta ƙarya

Ƴan sanda sun cafke waɗanda suka shirya yin garkuwa ta ƙarya

0

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta cafke wasu mutane 5 da ake zargi da shirya garkuwa da mutane na ƙarya, lamarin da ya shafi wani ɗalibi ɗan makaranta da abokansa huɗu domin yaudara da karɓar kuɗi daga iyayensa.

Rundunar ta bayyana kama mutanen ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta SP Abimbola Adebisi, ta fitar yau Juma’a.

Sanarwa ta ce, binciken farko ya nuna cewa lamarin, wanda ya tayar da hankalin jama’a, an fara kai rahotonsa ga ƴan sanda a matsayin ɓatan mutum a ranar 26 ga watan jiya Nuwamba.

Haka kuma, ta ce, An kama waɗanda ake zargin ne a ranakun 17 da 18 ga Disambar 2025, bayan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta inda aka ga yaron yana roƙon a tausaya masa, kamar yana cikin maɓoyar masu garkuwa da mutane.

Ta ƙara da cewa daga bisani bincike ya tabbatar da cewa garkuwar da ake iƙirari, yaron da abokansa ne suka shirya inda suka yi amfani da ɗakin ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin wajen aiwatar da wannan shiri.

Rundunar ƴan sandan ta ce, sun kama su ne a yankin Volkswagen Roundabout da kuma Ago Palace duk a birnin na Lagos.

Masu bincike sun ce waɗanda ake zargin sun shirya garkuwa da yaron ne domin karɓar kuɗi daga mahaifiyarsa mai suna Aligwo, wadda ta karɓi naira miliyan huɗu kwanan nan daga wata gudummawa.

SP Abimbola ta bayyana cewa mahaifiyar yaron har ta biya kuɗin fansa na naira miliyan 1 da dubu 700, inda aka tura kuɗin zuwa asusun ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, daga bisani kuma suka raba kuɗin a tsakaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here