Home Labarai Kano: An kama babban jami’in Kotu bisa dilmiyar da Miliyan 35 na...

Kano: An kama babban jami’in Kotu bisa dilmiyar da Miliyan 35 na Marayu a harkar Crypto

0

  An Kama Rijistaran kuɗi na kotun Musulunci bisa zarginsa da saka Naira Miliyan 35 na Marayu a  harkokin Crypto.

Babban magatakardar kotunan Musuluncin Alhaji Abubakar Haruna Khalil, ya tabbatar da rahoton a yayin da ya zanta da Premier Radio, inda ya ce, hukumar na gudanar da bincike ne domin tabbatar da gaskiyar zarge-zargen.

Haka kuma, Alhaji Khalil ya ce duk wasu matakai da za a ɗauka za su kasance cikin bin doka da oda, domin kare hakkokin marayu da tabbatar da gaskiya a harkokin kotunan Musulunci.

Binciken ya biyo bayan rahotannin da ke nuna almundahana da amfani da kudaden jama’a a harkokin saka jari marasa izini, lamarin da ya janyo hankalin hukumar kula da kotunan ɗaukaka kara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here