Home Labarai Matasa sun yi wa shugaba Tinubu ihu a Masallacin Juma’a a Abuja

Matasa sun yi wa shugaba Tinubu ihu a Masallacin Juma’a a Abuja

0

Wasu fusatattun matasa, sun yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ihun nuna rashin  amincewa da gwamnatinsa, jim kaɗan bayan kammala sallar Juma’a a Masallacin Shehu Shagari da ke Abuja.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026, yayin da shugaban ƙasar ke barin masallacin bayan gudanar da sallar Juma’a, inda wasu daga cikin masu ibada suka rika rera kalaman adawa da shi.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin mutanen sun rika cewa “Ba ma yi, ba ma so” a matsayin hanyar bayyana rashin gamsuwarsu da yadda al’amura ke tafiya a ƙasar.

Wasu daga cikin masu ibadar sun nuna rashin jin daɗinsu kan matakan tsaron da aka ɗauka yayin ziyarar shugaban ƙasar, inda aka ruwaito cewa an hana wasu shiga masallacin, yayin da aka takaita zirga-zirgar wasu masu ibada har sai shugaban ƙasar ya kammala ibadarsa ya bar wajen.

Sai dai fadar shugaban ƙasa ta musanta ikirarin cewa an kai wa ayarin motocin shugaban ƙasar hari, inda mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa na zamani, O’tega Ogra, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda Tinubu ke barin masallacin, yayin da wasu mutane ke yi masa kirari da gaisuwa.

Haka kuma, wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa an jefi ayarin motocin shugaban ƙasar, amma har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a samu cikakkiyar hujjar da ta tabbatar da cewa an jefi shugaban ƙasar ko kuma ya samu wani rauni ba.

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun ra’ayoyi mabambanta daga al’ummar Najeriya kan yadda gwamnati ke tafiyar da al’amuran ƙasar, musamman matsalolin tattalin arziki da sauran ƙalubalen da jama’a ke fuskanta.

Majiyoyi: Premium Times, Leadership, TheCable.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here