An sanya ƙarfe 10:00 na safiyar gobe Alhamis a matsayin lokacin yin jana’izar Marigayi Alhaji Sarki Aliyu Daneji ɗan majalistar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazaɓar Ƙaramar hukumar Birni KMC.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin ta Kano Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa, ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio yayin da ya ke tabbatar da rasuwar marigayin.
Lawan Hussaini, ya ce, tun da safiyar yau Laraba ne aka kai marigayin asibiti sakamakon rashin lafiyar da ke damunsa, sai dai daga bisani Allah ya yi masa rasuwa.
Haka kuma shugaban masu rinjayen, ya tabbatar da rasuwar ɗan majalisar dokokin mai wakiltar ƙaramar hukumar Ungogo Alhaji Aminu Sa’adu Ungogo.








