Home Labarai An yi jana’izar ɗan majalisar dokokin Kano Aminu Sa’adu Ungogo

An yi jana’izar ɗan majalisar dokokin Kano Aminu Sa’adu Ungogo

0

Da Almurun yau Laraba ne aka yi jana’izar marigayi Alhaji Aminu Sa’adu Ungogo, ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazaɓar Ungogo.

Marigayin ya rasu ne da yammacin yau sakamako yar gajeriyar jinya kamar yadda rahotonnni suka tabbatar.

Jana’izar tasa ta samu halartar ƙusoshin gwamnatin Kano da suka haɗa da gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo, da kwamishinoni har ma da jagoran jam’iyyar NNPP Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da dimbin al’umma da dama.

An dai gudanar da jana’izar marigayin ne a gidansa da ke cikin garin Ungogo a jihar Kano.

Kafin rasuwarsa, marigayi Alhaji Aminu Sa’adu Ungogo, shi ne shugaban kwamitin Kasafin kuɗi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here