Jami’ar Northwest Kano, ta kafa kwamitin bincike kan zargin da ake yi wa wani ma’aikacinta Dakta Nasa’i Muhammad Gwadabe, na yunƙurin cin zarafin wata ɗalibar Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria MAAUN.
A cikin wata sanarwa da jami’ar ta fitar yau Juma’a mai ɗauke dasa hannun shugaba sashe yaɗa labaranta Malam Abubakar Ibrahim.
Ta cikin sanarwar, jami’ar ta ce, ta samu labarin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ɗauke da zargin cewa lamarin ya faru ne a tsohon harabar Jami’ar Bayero Kano.
Jami’ar ta ƙara da cewa, ta na nuna matuƙar damuwa kan zargin, tare da jaddada cewa ba ta amince da duk wani nau’in cin zarafi, muzgunawa ko rashin ɗa’a daga ma’aikatanta ko ɗalibanta ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa an kafa kwamitin bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru da kuma miƙa rahotonsa ga mahukuntan jami’ar.
Ta kuma bayyana cewa idan binciken ya tabbatar da zargin, jami’ar za ta ɗauki matakin ladabtarwa bisa ƙa’idoji da dokokinta.
A ƙarshe, jami’ar ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji yaɗa jita-jita, tare da bai wa kwamitin damar kammala aikinsa








