Allah ya yi wa Sarkin Gumel da ke Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Muhammad Sani II, rasuwa.
Majiyoyi daga fadar Sarkin sun bayyana cewa, ya rasu ne a birnin Cairo na ƙasar Masar a yau Alhamis, inda ya ke yin jinya.
Kafar yaɗa labarai ta Solacebase, ta ruwaito cewa, An haifi marigayin ne a ranar 12 ga Disamban shekarar 1942.
Marigayin, wanda shi ne Sarkin Gumel na 16 ya rasu ya na da shekaru 83, inda ya ke dab da cika shekaru 84.
Haka kuma, ta ruwaito cewa, ya na ɗaya daga cikin sarakunan da su ka fi daɗewa kuma su ka fi daraja a Arewacin Najeriya.
Ya hau karagar mulki ne a ranar 16 ga watan Disamban shekarar 1980, bayan rasuwar mahaifinsa, inda aka ba shi sandar mulki a watan Mayu na shekarar 1981.
Marigayin dai, ya gudanar da mulki na tsawon fiye da shekaru 45.








