Home Ƙetare Amurka ta kai hari Venezuela tare da cafke shugaban ƙasar

Amurka ta kai hari Venezuela tare da cafke shugaban ƙasar

0

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce, ƙasarsa ta ƙaddamar da wani ”mummunan hari kan Venezuela” tare da “kama shugaban ƙasar, Nicolas Maduro” da matarsa.

BBC ta ruwaito cewa, shugaban ya bayyana hakan ne ta cikin wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce, a yayin harin an kama Shugaban ƙasar Nicolas Maduro da matarsa tare da ficewa da su daga ƙasar.

Trump, ya kuma ce, an ƙaddamar da harin ne tare da haɗin gwiwar jami’an Amurka.

Haka kuma ta ruwaito cewa, dama dai, Amurka ta jima tana barazanar kai hari Venezuela sakamakon tsamin dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, wanda ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here