Home Labarai Ƴan sandan Jigawa sun cafke Amarya bisa zargin kashe mijinta

Ƴan sandan Jigawa sun cafke Amarya bisa zargin kashe mijinta

0

Rundunar ƴan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wata amarya bisa zargin ta da kashe mijinta ta hanyar ba shi maganin ɓera a ƙauyen Gauza da ke ƙaramar hukumar Jahun ta jihar.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Alhamis, 23 ga Janairu, 2026, bayan mamacin ya ci abincin rana da aka ce matarsa ce ta shirya masa a gida.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da jama’a na rundunar, SP Shi’isu Adam, ya fitar a Dutse ranar Asabar, ya bayyana cewa bayan cin abincin, mijin ya kamu da matsananciyar rashin lafiya ba zato ba tsammani.

Sanarwar ta ce, an gaggauta kai shi asibiti domin samun kulawar likita, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa yayin da ake masa jinya.

“Bayan faruwar lamarin, jami’an bincike daga ofishin ‘yan sanda na Jahun sun fara gudanar da bincike, inda suka cafke matar mamacin a matsayin babbar wadda ake zargi,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa, “A yayin bincike, wadda ake zargin ta amsa laifin zuba gubar beraye a cikin abincin mijinta. Ta kuma bayyana cewa ta umurci ɗan uwanta ya sayo mata gubar da aka yi amfani da ita.”

SP Shi’isu Adam ya ce matar ta yi ikirarin cewa an tilasta mata yin auren ne daga iyayenta, lamarin da ta ce ya jefa ta cikin wannan aika-aika.

Ya ƙara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ta Jigawa ya bayar da umarnin a miƙa lamarin ga sashen binciken manyan Laifuka na Jiha SCID da ke Dutse domin zurfafa bincike.

Bayan kammala binciken, rundunar ta ce za a gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma yi kira ga jama’a da su zauna lafiya, su bi doka da oda, tare da neman hanyoyin shari’a da sulhu wajen magance matsalolin aure da na iyali.

Ta kuma gargadi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, tana mai jaddada cewa irin hakan kan haifar da sakamakon da ba za a iya gyarawa ba, tare da tabbatar da jajircewarta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

A halin yanzu, wadda ake zargin na tsare a hannun ‘yan sanda, tana jiran gurfanarwa a kotu.

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here