Rahotonni daga birnin Yenagoa na jihar Bayelsa, sun bayyana cewa, an shiga halin alhini da tsakar ranar yau Alhamis bayan fitar rahoton cewa mataimakin gwamnan jihar, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, ya yanke jiki ya faɗi, inda aka garzaya da shi cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke birnin na Yenagoa.
Lamarin ya faru ne kimanin ƙarfe 1:30 na rana a ofishinsa, lamarin da ya sa aka gudanar da ceton gaggawa domin kai shi sashen gaggawa na asibitin.
Ganau yayin faruwar lamarin, sun shaida wa manema labarai cewa, halin da ya ke ciki ya yi tsanani lokacin da aka isa da shi asibiti.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, ana kula da lafiyarsa a sashen kulawa ta musamman na cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Yenagoa.
Sai dai ba a samu wata sanarwa ta hukuma ba game da abin da ya haifar da matsalar lafiyar, sai dai majiyoyi sun ce yana iya alaƙa da matsalar zuciya.
Majiyar da ke kusa da mataimakin gwamnan ta danganta lamarin da yawan ayyukansa na yau da kullum, tana mai cewa yana yawan aiki fiye da kima, ya kamata ya ba kansa lokaci ya huta.
Haka kuma jaridar ta ƙara da cewa, jami’an tsaro sun mamaye harabar asibitin, yayin da manyan jami’an gwamnati suka ziyarci wurin domin nuna damuwa.







