Fadar Sarkin Musulmi, ƙarkashin jagorancin Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta ayyana gobe Litinin 22 ga watan Disamba, a matsayin ranar 1 ga watan Rajab na shekarar Musulunci ta 1447.
Shugaban kwamitin harkokin ƙoli na Addinin Musulunci na Fadar Sarkin Musulmin, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar kuma aka raba wa manema labarai a daren jiya Asabar, 20 ga watan Disamban shekarar 2025.
A cewar sanarwar, “Kwamitin ganin wata na fadar sarkin Musulmi ya tabbatar da cewa babu wani rahoton ganin watan Rajab da ya karba daga dukkan sassan Najeriya, saboda haka yau Lahadi, 21 ga watan Disamban Shekarar 2025, ta kasance 30 ga watan Jumada Thani na shekarar 1447 bayan hijirar Annabi Muhammad Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi”.
A don haka Sarkin Musulmin kuma shugaban majalisar koli ta addinin Musulunci NSCIA, ya aiyana gobe Litinin, 22 ga watan Disamban Shekarar 2025, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rajab.
Watan Rajab dai shi ne Wata na Bakwai a jerin watannin Musulunchi guda 12, wanda kuma hakan ke nuna cewa saura Watanni 2 a shiga Watan Ramadana.







