Gwamnatin Tarayya, ta tabbatar da cewa wasu tarkacen makamai na hare-haren da Sojin Amurka suka kai sansanonin ‘yan ta’addan ISIS sun faɗi a garin Offa na Jihar Kwara da kuma Jabo a Jihar Sokoto, yayin wani haɗin gwiwar aikin soja da Amurka da aka gudanar a ranar Juma’a.
A wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ya fitar, ya ce tarkacen makaman sun faɗi ne kusa da wani otal a Offa da kuma Jabo a Ƙaramar Hukumar Tambuwal, amma an tabbatar da cewa babu fararen hula da suka rasa rayukansu, kuma hukumomi sun gaggauta killace wuraren.
Haka kuma ya ƙara da cewa, Hare-haren sun mayar da hankali ne kan maboyar ‘yan ISIS da ke dajin Bauni a Ƙaramar Hukumar Tangaza ta Jihar Sokoto, inda aka aiwatar da su daga ƙarfe 12:12 na dare zuwa 1:30 a ranar 26 ga watan nan da muke ciki na Disamba, tare da amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Sanarwar ta ƙara da cewa an yi amfani da makamai masu bin GPS guda 16 ta jiragen yaki marasa matuƙa MQ-9 Reaper, bayan bayanan sirri sun nuna cewa wuraren da aka kai hari na zama cibiyoyin shirya hare-hare ne ga ‘yan ISIS da ke shigowa Najeriya daga yankin Sahel, lamarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a matsayin matakin kare al’ummomin Kirista daga hare-haren ‘yan ta’adda.







