Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin baɗi da ya kai kimanin naira Tiriliyan 1 da biliyan 477, bayan da kasafin ya zama doka a yau.
An gabatar da kasafin ne ga Gwamnan bayan amincewar da majalisar dokokin Kano, ƙarƙashin jagorancin shugabanta Jibrin Isma’il Falgore, tare da sauran ƴan majalisar.
Da ya ke jawabi bayan sanya hannu kan kasafin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa kasafin na baɗi, zai ba da muhimmanci ga bunƙasa tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya, noma da kuma ayyukan more rayuwa, domin inganta jin daɗin al’ummar jihar Kano.
Haka kuma, gwamna Abba Kabir Yusuf Ya kuma yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Kano bisa haɗin kai tare da duba kasafin akan lokaci, yana mai cewa hakan na nuna ƙudirin gwamnati da majalisa wajen tabbatar da ci gaban jihar.








