Majalisar Zartarwar Jihar Kano, ta amince da kashe kimanin Naira biliyan 6 da miliyan 900 domin yin manyan ayyukan hanyoyi, magudanan Ruwa da samar da ruwan sha da inganta ilimi, a wani yunƙuri na bunƙasa jin daɗin al’umma da haɓɓaka tattalin arziƙin jihar.
Majalisar ta yanke wannan shawara ne a taronta na 36 da aka gudanar a ranar 31 ga Disamba, 2025, a Gidan Gwamnatin Kano.
Da ya ke zantawa da manema labarai, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce, kuɗaɗen za su taimaka wajen hanzarta aiwatar da muhimman ayyuka a sassa daban-daban na jihar.
Daga cikin amincewar akwai ₦859.2m don biyan diyya a aikin gina hanyar kilomita biyar a Tudun Wada, ₦358.4m don magudanan ruwa a Kano Municipal, da kuma biliyoyin naira don sake gina hanyoyi da Kwalabati a Ƙiru da Nassarawa da sauran yankuna.
Haka kuma, majalisar ta amince da kuɗaɗe don ƙarfafa matasa ta hanyar koyon sana’o’i, faɗaɗa bututun ruwa a Gwale, da gina ajujuwa a ƙananan hukumomi 44 na jihar.
A ɓangaren dokoki, majalisar ta amince da tura muhimman kudurori zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano, tare da jaddada kudirin gwamnati na gaskiya, riƙon amana da ci gaba mai shigar kowa da kowa a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.








