Dakarun Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta tsaro JTF sun yi nasarar dakile yunƙurin wasu ’yan bindiga na shiga wasu yankuna a ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano, bayan an shafe tsawon lokaci ana musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.
Rahotonni sun bayyana cewa, artabun ya fara ne a daren ranar Alhamis zuwa wayewar Juma’a, inda ya shafi yankunan Yankwada, Babanduhu da wasu kauyuka makwabta a yankin karamar hukumar.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin ta hannun mai magana da yawunta a Kano Manjo Zubair Babatunde, inda ya bayyana faruwar lamarin ga manema labarai ya na mai cewa, ƴan bindigar sun yi ƙoƙarin shiga yankunan ne a kan babura suna harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa.
Sanarwar ta bayyana cewa harin ramuwar gayya ne sakamakon rasa wasu daga cikin ’yan bindigar a wani artabu da ya gabata, inda sojoji suka yi amfani da karfin makamai wajen dakile su.
Rahoton ya nuna cewa ’yan bindigar sun kutsa cikin kauyukan da misalin karfe daya na dare, lamarin da ya sa sojojin rundunar hadin gwiwa suka dauki matakin gaggawa domin kare al’umma.
Matakin da sojojin suka dauka cikin hanzari ya hana asarar rayuka da kuma barnata dukiyoyi a yankunan da abin ya shafa, tare da tabbatar da zaman lafiya a wuraren.
Rundunar sojin Najeriya ta jaddada cewa tana cikin shirin ko-ta-kwana domin hana sake faruwar irin wadannan hare-hare, tare da bukatar al’umma su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai ta hanyar samar da sahihin bayani a kan lokaci.
Solacebase








