Home Labarai Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan buƙatar belin Abubakar Malami

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan buƙatar belin Abubakar Malami

0

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 7 ga watan nan da muke ciki na Janairu domin yanke hukunci kan buƙatar beli da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN, ya gabatar mata a tuhumar da ake yiaaa ta almundahanar kuɗaɗe.

Tun a zaman kotun na baya ne dai Abubakar Malami ke tsare a gidan gyaran hali na Kuje bayan kotu ta bayar da umarnin tsare shi tun bayan gurfanar da shi.

Shari’ar ta shafi Malami tare da dansa Abdulaziz Malami wanda lauya ne mai mukamin SAN, da kuma daya daga cikin matansa Bashir Asabe, inda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gurfanar da su bisa tuhuma guda goma sha shida.

Ana zargin mutanen ukun da hada baki wajen wankiyar kudade har Naira Biliyan Takwas da Miliyan Ɗari Bakwai, lamarin da suka musanta lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen a gaban kotu.

Bayan sun yi watsi da tuhumar, Mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali na Kuje, tare da jinkirta sauraron bukatar belin zuwa ranar da aka sanya domin kotu ta yanke hukunci.

A cikin tuhumar da aka gabatar mai lamba FHC/ABJ/CR/700/2025, hukumar EFCC ta zarge su da ɓoye asalin kudaden da ake zargin sun samo asali daga ayyukan da ba su halatta ba, ta hanyar amfani da asusun bankuna daban-daban, kamfanoni da kuma sayen manyan kadarorin gine-gine tsawon kusan shekaru goma.

Rahoton tuhumar ya nuna cewa laifukan sun faru ne tsakanin shekarun 2015 zuwa 2025 a birnin tarayya Abuja, a lokacin da Malami ke rike da mukamin Antoni Janar na tarayya.

Hukumar EFCC ta kuma zargi Malami da dansa da amfani da wani kamfani domin boye kudade a asusun banki, tare da sayen kadarori da dama a Abuja, Kano da Birnin Kebbi, wanda ake zargin an yi su ne ta hanyar wakilai da kamfanoni domin ɓoye ainihin mallaka, abin da ake cewa ya saba dokokin yaki da almundahanar kuɗaɗe ta ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here