Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta sanar da ƙara wa’adin da ta bai wa jam’iyyu na gabatar ma ta da sunayen ‘yan takararsu na zaɓen 2027 da kwana uku.
ta cikin wata sanarwa da INEC ta fitar, ta ce jam’iyyu yanzu suna da damar miƙa sunayen ‘yan takararsu har zuwa tsakar dare na ranar 14 ga Yuli agogon Najeriya.
Hukumar ta bayyana cewa ta yanke wannan shawara ne bayan majalisar tuntuɓa ta jam’iyyun siyasa ta buƙaci hakan sakamakon ƙorafin fuskantar matsaloli wajen saka sunayen ƴantakarar a shafin yanar gizon hukumar.
A cewar INEC, ƙarin wa’adin zai ba bai wa jam’iyyu damar shiga tsarin zaɓe cikin sauƙi tare da tabbatar da bin tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta Najeriya.








